Tattaki domin jawo hankali kan sauyin yanayi
September 20, 2019Masu zanga zangar na bukatar shugabanin kasashen duniya wadanda za su hallara a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin New York su dauki matakan da suka dace domin shawo kan mummunan bala'in da sauyin yanayin zai iya haifarwa ta hanyar rage gurbataccen hayakin masana'antu nan da shekara ta 2030.
Batun sauyin yanayi dai ya zama batu mai sarkakakiya a Australia mai arzikin kwal inda gwamnatin ta 'yan ra'ayin rikau ta kafe wajen kin daukar matakai domin magance sauyin yanayi.
Za a gudanar da makamacin wannan zanga zangar har fiye da 5,000 a kasashe fiye da 156 a wannan Juma'ar.
Tattakin ya zo daidai da kudirin da wata matashiya 'yar kasar Sweden mai shekaru 16 da haihuwa Greta Thunberg ta dabbaka wadda za ta jagoranci zanga zangar lumana zuwa hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya inda shugabanni za su tattauna yiwuwar sauyi daga makamashin da ake amfani da shi yanzu zuwa sabbin dabarun makamashi mara gurbata yanayi.