1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

An yi fito-na-fito kan sakamakon zaben Amirka

December 13, 2020

An samu yamutsi a birnin Washington na Amirka biyo bayan 'karon-battan' da aka yi a tsakanin masu zanga-zanga magoya bayan Shugaba Donald Trump mai barin gado da kuma wasu masu ra'ayin rikau da ake kira Proud Boys.

https://p.dw.com/p/3mdwa
USA Proteste und Ausschreitungen in Washington
Hoto: David Ryder/Getty Images/AFP

Masu zanga-zangar na Trump da suka yi wa gangamin nasu lakabi da 'Stop The Steal' na ci gaba da korafi kan zargin magudin da suka ce an yi wa Donald Trump.

Mr. Trump ya samu labarinsu, kuma ya sanya an tuka sa ta jirgin sama domin ratsawa ta samansu yadda za su san yana tare da su. Kazalika ya kuma jinjina musu a shafinsa na Twitter.

Wannan na zuwa ne a yayin da kotuna na jihohi da ma na tarayya a Amirka suka yi watsi da bukatar Trump ta a sauya sakamakon zaben. A wannan Litinin  mai zuwa ce kuma wakilan masu zabe za su zauna domin kara tabbatar da nasarar da Joe Biden ya samu kan Shugaba Trump.