An kama ministan kudin Kenya kan zargin cin hanci
July 23, 2019Ana sa ran gurfanar da Henry Rotich ministan kudin kasar Kenya a gaban kotun musamman da aka kafa kan yaki da cin hanci da rashawa. An cafke ministan da hukumomin kasar suka bayyana cewar ana tuhuma bayan da 'yan sanda suka gudanar da bincike kan yadda aka yi da kudin da aka ware domin aikin wanda aka baiwa wani kamfanin kasar Italiya kwangila.
Akwai kuma wasu mutane takwas da ake zargin suma suna da hannu a wannan badakala kuma a halin yanzu za su fuskanci shari'a kan laifuka na kokari wajen wawashe dukiyar jama'a sai dai ministan da mutanen sun musanta wannan zargi.
Shi dai Henry Rotich ministan kudin kasar Kenya ya kasance babban jami'i na farko da aka kama kan tuhumar cin hanci a wannan kasa da ake zargin manyan jami'an gwamnati da wadaka gami da babaketre da duniyar gwamnati.