Angola: An fara gudanar da babban zabe
August 22, 2017A wannan rana ta Laraba ce al'ummar kasar Angola ke fita kada kuri'a domin zaben sabon shugaban kasa da zai maye gurbin Shugaba Jose Eduardo Dos Santos da ya kwashe shekaru 38 kan karagar mulki, sai dai har yanzu ana ganin jam'iyyar shugaban ta MPLA ita za ta sake kaiwa ga karagar mulki duk da matsaloli na tattalin arziki da kasar ke fiskanta.
Jam'iyyar ta MPLA dai ita ke mulkin wannan kasa ta Angola tun bayan da ta samu 'yancin gashin kanta daga kasar Portugal a shekarar 1975. Janyewar ta Shugaba Dos Santos ba zato ba tsammani dai ko da yake akwai dalilai na rashin lafiya ana mata kallon wata dama ta samar da sauyi a siyasar kasar da ke a kan gaba wajen fitar da albarkatun man fetir a nahiyar Afirka.
Joao Lourenco ministan tsaro dan gani kashenin Dos Santos da ake ganin zai gaji shugaban ana ganin da wahala ya kauce daga tsarin gwamnatin shugaban mai barin gado da ta yi suna a harkoki da suka shafi cin hanci da rashawa da ta gaza kawar da mugun talauaci a tsakanin 'yan kasa. Tun daga misalin karfe bakwai na safiyar nan ce dai aka bude tashoshin kada kuri'ar da za su dauki tsawon sa'oi 11.
Babban abin da ya karawa jam'iyar MPLA karfi shi ne rashin hadin kai daga 'yan adawar kasa, inda jam'iyyar UNITA ta 'yan tawaye da ta rikide zuwa jam'iyar siyasa ke karkashin jagorancin Isaias Samakuva, sannan Abel Chivukuvuku ke zama shugaban jam'iyyar CASA-CE wacce aka kafa a shekara ta 2012. A baya Dos Santos ya sha suka kan yadda ya ke bai wa 'yan uwa da 'yan siyasa da ke da kusanci da shi fifiko a gudanar da harkokin mulki.