Angola: Dos Santos ya yi bankwana da siyasa
September 8, 2018Bayan shekaru kusan 40 yana jagorancin kasar da ma jam'iyyar ta MPLA "Mouvement Populaire de Libération de l'Angola", Dos Santos a yanzu ya bar ragamar shugabancin jam'iyyar a hannun wanda ya canje shi Joao Lourenço. Dan shekaru 76 da haihuwa Dos Santos ya sanar da sauka daga jagorancin jam'iyyar a gaban wakillai sama da 300 da suka fito daga sassa dabam-daban na kasar a wani babban zaman taron gaggawa da jam'iyyar ta kira a Luwanda babban birnin kasar ta Angola.
Shi dai José Eduardo dos Santos ya jagorancin kasar ta Angola tun daga shekara ta 1979 zuwa 2017, inda a bara ya sanar cewa ba zai sake tsayawa takara ba sabili da fama da yake yi da rashin lafiya. Dos santos ya ce bai taba son wannan mukami na shugabancin jam'iyyar ba, kuma bai taba tsammanin zai rike shi har na tsawon lokaci ba, sai dai kawai wasu dalillan da suka haddasa hakan.