Angola: Joao Lourenco ya cika kwanaki 100
January 8, 2018Talla
Lourenco da ke kokarin kawo sauyi a harkokin mulkin kasar Angola ya ci karo da kalubale na rashawa musanman bayan da ya kori Isabel Dos Santos 'yar magajinsa daga mukaminta na shugabancin kamfanin mai da kuma shirin sauke dan shugaban daga mukaminsa da ya ce zai yi in har bukatar hakan ta taso.
Tuni dai batun ya soma haifar da cece-ku-ce a tsakanin al'umma ganin har wasu dake da kusanci da tsohon shugaban ba su tsira ba tun bayan hawansa mulki, sai dai kuma shugaban ya ce ya na aikinsa ne kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi damar yi a jawabinsa na wannan Litinin ga al'umma a yayin taron cika kwanaki dari da soma mulkin kasar da kusan akasarin al'umma suka sani da shugaba daya tilo da ya kwashi kusan shekaru arba'in ya na mulki.