Angola: Joao Lourenço ya sha alwashin yaki da cin hanci
July 26, 2017Lourenço ya yi wadannan kalamai ne ya yin wani taron gangami na jam'iyyarsa ta MPLA ta shirya a yakin neman zaben da aka soma na zaben 'yan majalisar dokokin kasar da zai gudana a ranar 23 ga watan Augusta mai kamawa.
Shidai Joao Lourenço mai shekaru 63 da haihuwa, shi ne kan gaba cikin jerin sunayen 'yan takara na jam'iyyar ta MPLA ta shugaban kasa Jose Eduardo Dos Santos wanda ya zabi kin sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar bayan da ya shafe shekaru 37 ya na mulkin kasar ta Angola.
Kundin tsarin mulkin kasar ta Angola dai bai tanadi zaben shugaban kasa ba, sai dai jam'iyyar da ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokoki ce ke da shugaban kasa. Baya ma ga yaki da cin hanci, dan takaran jam'iyya mai mulkin ya sha alwashin rarraba arzikin kasar daidai wadaida ga sauran yankunan, da kuma bunkasa harkokin kasuwanci idan har ya yi nasara.