Angola ta fitar da jadawalin zaben gama gari
April 25, 2017Yayin wani taron manema labarai da ya jagoranta ne, babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Angola Joao Maria de Sousa, ya ce bisa shawarar shugaban kasa, babbar majalisar jamhuriya ta kaddamar da jadawalin zabukan gama gani na kasar ta Angola. Wannan mataki zai kawo karshen wa'adin mulki na shekaru 30 da shugaba Dos santos ya yi yana mulki.
Shugaban na Angola dos Santos mai shekaru 74 da haihuwa, na a kan karagar mulkin kasar ne tun daga shekara ta 1979, inda ya ce ba zai sake neman wani wa'adin mulki ba. A watan Febirairu da ya gabata ne dai jam'iyyarsa ta MPLA ta zabi ministan tsaron kasar na yanzu José Lourenço a matsayin wanda zai gaje shi. Masu adawa da shugaban kasar dai na zarginsa da yin abun da ya ga dama da dukiyar kasar.