1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar cutar shawara a kasar Angola

Salissou BoukariFebruary 15, 2016

Hukomomin kiwon lafiya a Angola sun sanar da barkewar cutar zazzabin shawara wadda kawo yanzu ta yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

https://p.dw.com/p/1HvqO
Afrika Kinderkrankenhaus in Malanje, Angola
Hoto: DW/N. Sul D'Angola

Annobar cutar Shawara ta yi sanadiyar rasuwar mutane akalla 51 daga cikin mutane 240 da suka kamu da cutar a kasar Angola tun daga ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata kawo yanzu. Wannan annoba dai ta fi kamari ne a yankin karamar hukumar Viana da ke kauyen Luanda babban birnin kasar, inda nan kadai aka samu rasuwar mutane a kalla 29 daga cikin mutane 92 da suka kamu da cutar a cewar babban darectar kiwon lafiyar ta kasar Adelaide de Carvalho.

Tuni dai hukumomin kiwon lafiyar suka tsunduma cikin allurar rigakafin wannan cuta inda aka samu yi wa mutane akalla dubu 451 daga cikin mutane miliyan daya da dubu dari biyar da ake son yi wa annurar a wani mataki na takaita yaduwar cutar.