1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda na tsananta hare-hare a Kaduna

Ibrahima Yakubu AMA(Lateefa)
June 28, 2022

Wata kungiyar 'yan ta'adda ta karbe iko da wasu sassan yankin birnin Gwari na jihar Kaduna a arewacin Najeriya, inda ta haramta jama'a gudanar da duk wasu taruka na siyasa.

https://p.dw.com/p/4DN9u
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Kungiyar 'yan ta'adda ta Ansaru da ke cigaba da mamaye yankunan gabashin karamar hukumar birnin Gwari ta jihar Kaduna ta haramta gudanar da tarukan siyasa da sauran duk wasu lamuran da suka shafi tallata ‘yan takara a yankin baki daya.

Malam Ishaq Usman shugaban hadaddiyar kungiyar ci-gaban masarautar birnin Gwari ya fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da haka, yana mai cewa daukacin mazabu bakwai daga cikin 11 na yankin gabashin birnin Gwari na karkashin ikon 'yan bindigar Ansaru. 

Karin Bayani: Rashin tabbas ga rayuwar al'ummar Najeriya

Kungiyar fafutikar kare da dimukuradiyya da dorewarta "Nigeria Campaign for democracy" na nuna bacin ransu tare da bayyana hakan a matsayin wani abin takaici in ji Abdul Bako. "Yadda ake samun kungiyoyin 'yan ta’adda ke yaduwa na kara zama babbar barazana ga zaman lafiyar kasa da dorewar mulkin demokuradiyya."

Kungiyoyin fafutikar dorewar dimukuradiyya na jan hankalin gwamnatoci kan daukar manyan matakai da ya kamata cikin gaggawa don magance yadda mutane galibi matasa ke bin ra'ayoyin 'yan ta’adan Ansaru, da rashin magance matsalar ka iya kara zama wani kalubale muddin hukumomi da sauran kungiyoyin ba su hanzarta daukar matakan da suka dace ba akan lokaci.

Karin Bayani: ‘Yan bindiga na yawo da rana tsaka a Najeriya 

Gwamnatin jihar Kaduna ta koka bisa yadda ‘yan ta’addan yankin Kudu maso gabashin Najeriya irin Boko Haram da ISWAP da Ansaru suka dawo a jihar ta Kaduna, lamarin da ke kara tayar da hankalin mazauna jihar.