Arangamar Isra'ila da Falisdinawa
December 28, 2011Talla
An sake samun dauki-ba-dadi tsakanin Isra'ila da mayakan Falisidinu wanda a cikinsa Isra'ila ta yi luguden wuta sau biyu a zirin Gaza. Likitocin masu ba da taimakon gaggawa a yankunan Falisdinawa sun ce mutun daya ya mutu wasu kuma su 12 sun samu raunuka. Ma'aikatar sojin Isra'ila ta jadadda cewa wani rukuni na 'yan ta'adda da ka iya shirya kai hare hare akan iyakar Isra'ila da Masar da ke yankin Sinai ne aka nufa da wannan harin. A ranar Litinin 26-12-2011 Falisdinawa su harba roroki guda biyu zuwa cikin kudancin Isra'ila. To ama babu wanda ya mutu ko ya samu rauni.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu