Argentina ta amince da dokar zubar da ciki
December 30, 2020Talla
'Yan majalisar dattawa 38 suka amince da dokar yayin da 29 suka kada kuri'ar rashin amincewa. Sabuwar dokar za ta bada damar zubar da cikin da ya kai mako 14.
Dubban jama'a sun yi dandazo a kofar majalisar dattijan da suka hada da masu adawa da kuma masu goyon bayan dokar. Fafaroma Francis wanda dan Argentina ne ya nuna rashin gamsuwa da dokar a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter.
Kafin wannan lokaci dai ba a yarda a zubar da ciki ba a Argentina sai da dalili mai karfi kamar fyade ko kuma idan rayuwar uwar na cikin hadari.