Asarar rayuka a yake-yaken kasar Libiya
May 21, 2015Talla
Akalla sojoji goma sun rasu tun a ranar Laraba a wani dauki ba dadi da aka yi a birnin Bengazi, yayin da wasu 36 suka samu raunuka. Sannan kuma an kashe wani mayakin kungiyar Fajr Libiya a kusa da birnin Misrata a wani harin da kungiyar IS reshen kasar ta Libiya ta dauki alhakin kaishi.
Birnin na Bengazi da ke a matsayin cibiyar tada kayar baya a kasar ta Libiya, na fuskantar matsalar yake-yake tun bayan rushewar gwamnatin marigayi Moammar Kadhafi a shekarar 2011. A tsawon shekara guda fadan na Bengazi ya haddasa rasuwar mutane fiye da 1700 tare da ficewar wasu miliyoyin mutanen don tsira da rayukansu.