Asusun UNICEF ya soki rashin kulawa da yara
February 28, 2012Babban abinda ake fata ga manyan birane dai shine su samarwa matasa makarantu, kiwon lafiya, kana idan yaran sun girma a basu wuraren aiki. Amma abun kaito shine 'ya'yan talakawa basa cin ribar irin waɗannan ababen more rayuwa da yakamata yara suma daga manyan birane. Usman Shehu Usman ya ya yi natsari kan rahoton da Asusun kula da yara annan ta MDD wato UNICEF ta fitar bisa takaicin da yara ke fiskanta a manyan birane
Samar da ingantaccen ruwan sha, makarantu, kulawar likitoci, da kuma aikin yi, idan yara sun girma, wannan shine abinda mahukunta, ingantattun ababen mure rayuwa, wadannan sune abinda ake fatan samu a birane. don baiwa yara damarsu kasance manyan gobe da asa zata dogara dasu. Amma abun kaito shine, aksarin aksarin birane a duniya, idan kaga yaro ya samesu to biya ya yi da kudinsa. Yara dake rayuwa a anguwannin marasa galihu, akasari suna tafiya ne kusan a galabaice. Kamar yadda rahoton asusun kula da yara na MDD wato UNICEF ya gano, inji Sarah Crowe kakakiyar asusun.
"A da dai a al'adance anfi samun talauci a karkara, amma yanzu lamarin ya sauya. Talauci na karkara, amma ya yi kanta birane ma. Shin wane mataki muka ɗauka, mi za mu yi a kai, wannan shine abinda rahoton ya maida hankali a akai"
Babu dai wani cikakken adadin alƙaluman yaran da ke tashi cikin irin wannan rayu a birane. Yara da yawa da ake haifuwa a birane, suna girma cikin wannan rayuwar talauci, ba tare da hukumomi sun kula da su ba. Mutannen da hukumomi basu son da su ba, babu yadda za a yi su samu ilimi ko kiwon lafiya. Inji Crowe
"Abinda muka gano a wannan rahoton shine, birane sun gaza wajen kula da yara. Abinda muke zato shine wajen kulawa da rayuwar yara, basa samar musu da ababen more rayuwa. An hanawa yara yancin su, talauci ya mamaye karkara da birane a faɗin duniya"
Rahoton shekara-shekara da asusun UNICEF ya fitar, ya nuna mummunar alama. Akasarin matalauta dai na rayuwane a anguwannin da gidajen da basa cikin doka, don haka a duk lokacin da gwamnati ta buƙaci filayen tana iya tura manyan motocin buldoza su rusa gidajen talakawa. A irin wadannan anguwanni an fi samun yan ɓata gari, kana yara 'yan shekaru 13 ana sa su ayyuka munana da suka hada da karuwanci da sauransu. a Faɗar Albert Recknagel jami'i a ƙungiyar kare yancin yara ƙanana.
"A gaskiya irin waɗannan yara ake samu a fadin duniya, waɗanda ke fadawa cikin munanan ayyukan acca. Suna fadawa shaye-shayen muggan ƙwayoyi. Kuma basu da wata makomar da birane suka shirya musu"
Wannan rayuwar cikin ƙunci da yara ke fuskanta dai bawai ga ƙasashe masu tasowa kawai take ba, amma a ƙasashen da suka ci gaba ma ba'a yin wani kekkawan shiri kan yara. Asusun UNICEF dai ya bada shawar cewa, dole a inganta yara dake rayuwa a anguwannin marasa galihu, kana hukumomi su tashi haiƙan wajen samarwa yara ababen mure rayuwa, walau a karkara ko birane.
Mawallafa: Helle Jeppesen / Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu