Asusun UNICEF ya yi kira da a kara taimakawa ´yan gudun hijirar Darfur
June 20, 2006Mia Farrow ta halarci gun taron ne a cikin wata riga shigen ta masu karamin karfi ba tare da ta sha kwalliya ba. Sau biyu cikin shekara daya da rabi jakadiyar ta UNICEF kuma ´yar wasan kwaikwayo ta ziyarci yankin na Darfur mai fama da rikici. Ta bayyana halin da ake ciki a yankin da cewa mawuyaci ne kuma mai ban tsoro. Rayuwar mutane kimanin miliyan 3 ta dogara kacokan akan taimakon ruwan sha, abinci da kuma magunguna daga kungiyoyin ba da agaji
“Ta ce UNICEF da wasu kungiyoyin ba da taimakon ne kadai suke tallafawa mutane a yankin Darfur. A gaskiya in ban da wannan babu wani taimako kuma da suke samu.”
A ma halin da ake ciki wannan taimako na cikin wani hadari. Alal misali yankunan yammacin kasar inda ta kaiwa ziyara watanni 18 da suka wuce a wannan karon jakadiyar ta UNICEF ta kasa shiga wannan yanki saboda hadarin da ke ciki. Yanzu haka an shiga wani mummunan hali na rashin sanin tabbas tun da aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin ´yan tawaye akan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da gwamnatin birnin Khartoum. A wuraren da ta iya kaiwa ziyara kuwa an dan samu ci-gaba domin an samarwa ´yan gudun hijirar bukkoki mai maimakon kwana a karkashin bishiyoyi. To amma a tilas kungiyoyin agaji na bari manyan wurare, inji shugaban UNICEF a Jamus Dietrich Garlichs.
“Ya ce halin na kara yin muni ne saboda a wannan shekara ba kamar a farkon barkewar rikicin ba, kungiyoyin agajin ba sa samun taimako. A bana kashi 20 cikin 100 na kayan da UNICEF ke bukata ga wannan shekara, ya samu.”
A nata bangaren Mia Farrow ta soki gwamnatocin kasashen yamma da rashin ba da isasshen taimako ga rundunar kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayar Afirka ta tura a yankin, bayan su din ne suka matsa lamba na hada kan wannan runduna. Dan ta wato Ronan Farrow wanda shine jakadan matasa na asusun UNICEF da dafawa mahaifiyarsa baya a wannan ziyara a Darfur. Ya tofa albarkacin bakinsa yana mai cewa:
“Ya ce Idan jama´a suka matsawa gwamnatocin su lamba da su dauki sahihan matakan warware wannan matsala ta hanyar siyasa, to ko shakka babu za´a samu mafaka.”
Ita ma Mia Farrow ta jaddada cewar idan aka matsa lamba ta fannin siyasa to za´a warware rikicin na Darfur wanda hakan zai kawo karshen wahalhalun da mutanen yankin ke sha. Ta ce idan gamaiyar kasa da kasa ba ta yi hobasa yanzu ba to ba bu wata makoma mai haske ga ilahirin al´umomin Darfur musamman yara kanana.