1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta baiyana damuwa akan rikicin Sudan da Sudan ta kudu

April 11, 2012

Kungiyar gamaiyar Afirka AU ta umarci sudan ta kudu ta janye sojojinta daga yankin Heglig

https://p.dw.com/p/14bp8
An SPLM-N fighter sits on a camouflaged truck at the bush camp of the rebel movement’s leader, Malik Agar. Copyright: Jared Ferrie, DW freier Mitarbeiter, Kurmuk, Sudan October 2011
Hoto: DW

Kungiyar gamaiyar Afirka ta baiyana matukar damuwa da mummunan tarzomar dake ruruwa a tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu. Kungiyar ta kuma yi kira ga Sudan ta Kudu ta janye sojojinta daga yankin Heglig, tana mai umartar kasashen biyu su nuna halin dattako. Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta ce kutsen da Sudan ta Kudu ta yi a cikin kasarta shine lamari mafi muni tun bayan da Sudan ta Kudu ta sami yancin kai a watan Yulin bara. Kakakin rundunar sojin Sudan Kanar Sawarmy Khaled yace sojin Sudan ta Kudu sun kwace babbar rijiyar man Sudan dake garin Heglig mai tazarar kilomita 100 daga gundumar Abiyei. Bangarorin biyu sun tafka yakin basasa wanda aka shafe shekaru da dama. A yanzu dai dukkan kasashen biyu na umartar fararen hula su yi kokarin kare kansu da iyalansu abin da ke haifar da fargabar sake barkewar wani yakin a tsakanin su.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh