Ayatollah Ali Khamenei ya zargi Amirka da Isra'ila da hura rikicin Siriya
August 31, 2012A dabara ga taron kasashe 'yan ba ruwan mu da a ke gudanarwa a kasar Iran wanda kuma a ke saran kamala shi a wannan Juma'ar,jagoran juyin juya halin kasar Ayatollah Ali Khameine,ya zargi fadar Amurka da kasar Isra'ila da zama masu hura rikicin kasar Siriya a bayan fage. Ali Khamenei ya ce rashin gano bakin rikicin kasar ta Sirya ya samo tushensa ne ga kasashen biyu da ke tura dubban makamai da kudade ga 'yan adawan kasar. Jagoran ya yi wannan furucin ne a yayin ganawarsa da pramiyan kasar Siriya Wael Al-Halaqi a yau juma'a. Baya ga haka kuma ya yi watsi da rahoton hukumar kasa da kasa ta AIEA ta kula da makamashi wadda ta zargi hukumomin na Iran da hanawa jami'anta ziryatar tashoshin nukleyarta da ke Parchin. Kasashen yamaci da Isra'ila na zargin kasar ne da yunkurin kera makaman nukleya xa boye yayyinda kasar ta ce tashoshinta na muradun farar fulla ne kawai.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mahamadou Awal Balarabe