Sudan: Najeriya ta fara kwashe 'yan kasarta
April 26, 2023Ayerin farko na dubban 'yan Najeriyar da aka fara kwashewa ya kunshi dalibai da ke karatu a jami'o'in Sudan kuma an fitar da su daga kasar ne a cikin motocin bus bakoye domin kai su Masar inda daga can ne za a kwashesu a jiragen sama izuwa Abuja babban birnin Tarayya.
Jim kadan bayan tashin ayerin farko shake a cikin motocin bus izuwa birni Assouan na Masar, kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, Manzo Ezekiel ya shaidawa kanfanin dillanci labaran Faransa na AFP cewa an tanadi motocin bus sama da 50 domin jigilar 'yan Najeriya 3.500 daga cikin 5.000 da suka makale a Sudan din tun bayan barkewar rikicin a ranar 15 ga watan Aprilu. Ya kuma kara da cewa daga kasar Masar din kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Air Peace mallakar Najeriya shine ya dauki nauyin isa da su izuwa Abuja kyauta ba tare da biyan wasu kudade ba.