1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon jin kai na fuskantar tarnaki a Sudan

May 4, 2023

Ana ci gaba da fuskantar wahalhalun jin kai a kokarin kare rayukan fararen hula na Sudan da rikici ya ritsa da su a kan hanyarsu ta ficewa daga kasar.

https://p.dw.com/p/4QuV1
Hoto: Gueipeur Denis Sassou/AFP

Rania Abdelaziz, wata 'yar gwagwarmayar Sudan ta bar babban birnin Sudan, Khartoum, gabanin fafatawar da ake yi domin gudanar da azumin watan Ramadan tare da iyalanta a birnin Alkahira. Ta shaida wa tashar DW cewar har yanzu duniya ba ta yi la'akari da mummunan halin jin kai da kasarta ke ciki ba.

A tsakiyar watan Afrilu ne fada ya barke tsakanin manyan hafsoshin soja biyu Abdel-Fattah Burhan da Mohammed Dagalo, wanda aka fi sani da Hemeti, matsalar da ta sa Rani Abdelaziz yanke shawarar ci gaba da zama a Masar na wani lokaci, da kuma taimaka wa'yan gudun hijirar Sudan da ke zuwa Masar din.

Karamin ofishin jakadancin kasar Masar na ci gaba da bayar da bizar yawon bude ido ga ‘yan Sudan da ke son tsallaka kan iyaka, duk da ruruwar rikicin da ya yi sanadin jikkatar mutane kusan 5,000 tare da kashe akalla mutane 550, a cewar alkaluman ma'aikatar lafiya ta baya-bayan nan, wadanda ake ganin ma za su iya fin hakan.

Hager Ali, wata mai bincike a cibiyar nazarin GIGA ta Jamus ta shaida wa DW cewar akwai manyan matsaloli na tsarin mulki da na gudanarwa a bangarorin biyu wato iyakar Sudan da Masar, don aiwatar da takardun da suka dace don samun damar shiga Masar bisa ka'ida, kuma babu wata takardar izinin shiga Masar a wannan lokaci daga bangaren mahukuntan birnin Cairo.

Ali ta ce "Lokacin da aka kwashe ma'aikatan diflomasiyya daga Sudan a farkon wannan rikicin, an dakatar da batun neman biza da duk wani batu na takardun fasfo da sauran muhimman takardun tafiye-tafiye, kuma tun daga lokacin matsalar ta kasance haka".

A halin da ake ciki kuma lamarin ya kara tabarbarewa a kan iyakar Sudan da Masar ta cikin ruwa, inda dubban mutane suka kafa sansani a wajen tashar jiragen ruwa da ke tsakanin kasashen biyu. Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta sanar a farkon makon nan cewa, za ta kaddamar da wani shiri na mayar da martani ga hukumomin Sudan da Masar tare da gaggauta karkatar da kayayyakin agaji daga Chadi da Sudan ta Kudu.