Ba abin da zai shafi huldar Amirka da Saudiyya
November 21, 2018Shugaba Trump ya yi wannan furuci ne a wata fira da manema labarai a jiya Talata bayan da aka tambaye shi ra'ayinsa dangane da bayanan da hukumar leken asirin kasarsa ta CIA ta yi da ke cewa babu tababa Mohamed Ben Salmane ne ya kitsa kisan dan jaridar.
Shugaba Trump ya ce babu wani tabbacin a cikin binciken da hukumar ta CIA ta yi. Ya kuma kara da cewa babu tabbacin yariman na da masaniya kan kisan dan jaridar, amma kuma ya ce ala kullin halin suna tare da Saudiyya kuma za su ci gaban da kasancewa tare da ita.
Shugaba Trump dai ya bayyana wannan matsayi nasa ne daidai lokacin da yake shan matsin lamba daga ko'ina domin ganin ya dauki mataki kan Saudiyya dangane da batun kisan dan jaridar. Wadannan kalamai na Shugaba Trump a game da batun kasar ta Saudiyya dai sun fuskanci suka har daga jam'iyyarsa ta Republicain.