Batun tsaro da makomar ma'aikata a taron CDTN
September 20, 2022Bayan kowane shekaru hudu kungiyar kwadago ta CDTN na gudanar da babban taron Congres da a ciki take sabunta mambobin kungiyar bayan samunn amincewar wakillai da suka fito daga sassa dabam-dabam na Nijar.
Ministar kula da harkokin ma'aikata Hadizatou Kafougou ta jinjina wa mahalarta taron, tare da cewa "Batun zaman lafiya da tsaro na kan gaba ga tsarin aikin da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, sannan gudunmowar da kungiyoyin kwadago za su bayar na da mahimmanci ga gwamnatin Nijar."
Wakillai daga kungiyoyin kwadago kamar CGT da CFDT na Faransa da CSA da CGTB da UNSTB da CSTB CSA daga Jamhuriyar Benin da Senegal da Mali sun halarci bikin bude taron.
Jean-Baptiste Callebout na kungiyarsu CGT ta Faransa ya nuna irin yadda kungiyar ke adawa da tsarin jari hujja da Faransa ke nunawa a cikin kasashen Afirka, ya kara da cewa "Zan so wannan taro na kungiyar kwadago ta CDTN ya bada matsayinsa kan kasancewar sojojin na Faransa a Nijar domin mu kuma mu bada cikeken bayani ga kungiyarmu ta CGT a Faransa."
A tsawon kwanaki uku hadaddiyar kungiyar CDTN mai mambobi 54, za ta tattauna kan wasu batutuwan da suka dauki hankulla a siyasar kasashen Afirka da ma na Turai