Babu wata yarjejeniya kan nukiliyar Iran
November 24, 2014Sassan biyu sun kwashe akalla shekaru 12 suna ta takaddama a kan batun nukiliyar kasar ta Iran. Tuni ma dai kasashen suka fara tunanin kara wa kansu lokaci domin daddale batun na nukiliyar Iran bayan da a wannan Litinin suka shiga rana ta karshe ta wa'adin da aka debar musu domin su cimma yarjejeniya, ba kuma tare da sun samu matsaya a tsakaninsu ba.
Makasudin tattaunawar da suke yi a birnin Vienna dai shi ne samun mafita da za ta kawo karshen takunkumin karya tattalin arzikin da Iran ta kwashe shekaru a cikinsa, wanda kuma ya sanya tattalin arzikin kasar shiga cikin halin tsaka mai wuya. A jawabin da ya yi ga manema labarai, minsitan harkokin kasashen waje na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce har yanzu akwai gagarumin gibi tsakaninsu da Iran a kan muhimman batutuwa da suka gaza samo mafita.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe