1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure da dama sun mutu a Libiya

Suleiman Babayo
January 6, 2018

A karon farko cikin wannan shekara ta 2018 fiye da bakin haure 30 ne da ke neman zuwa kasashen Turai ne suka hallaka a gabar tekun Libiya.

https://p.dw.com/p/2qRQg
Libyen (Symbolbild) afrikanische Migranten auf Rettungsboot
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Palacios

Sojojin ruwa na Libiya sun ce mutanen kimanin 25 sun hallaka ne lokacin da jirgin ruwan da suke ciki ya samu matsala, kamar yadda mai magana da yawun sojojin ruwa na kasar ya bayyana.

A wani labarin kuma, masu gadin gabar tekun Italiya sun tsamo gawar wasu mutanen takwas tare da ceto bakin haure 84 a cikin tekun Bahar Rum. Bakin hauren dai sun fito ne daga kasar Libiya a kan hanyarsu ta zuwa Turai. Wani jirgin sama da ke sintiri a kan tekun ne ya gano bakin hauren da suka shiga mawuyacin hali.

Wannan ne dai ke zama karo na farko cikin sabuwar shekara ta 2018 da muke ciki, da aka tababatar da samun wadanda suka mutu a cikin teku a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai. Fiye da bakin haure 3,100 ne suka rasa rayukansu a shekarar da ta gabata ta 2017 a cikin teku, a kan hanyar zuwa nahiyar Turai galibi wadanda suke bi ta kasar Libiya, wadda ta fada cikin rikici tun shekara ta 2011 bayan kifar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.