Bana babu zabe a Sudan ta Kudu
March 24, 2015Majalisar dokokin Sudan ta Kudu ta kada kuri'ar da ta amince da kara wa'adin jagorancin shugaba Salva Kiir da shekaru uku, abin da ya soke duk wani shiri na yin zabe a cikin wannan shekarar kamar yadda aka zata tun farko, a kasar da ta shafe watanni tana fama da rikici.
Wannan mataki dai, masu nazarin lamuran kasar sun ce zai kawo tangarda ga yunkurin masu shiga tsakani a yankin, wadanda suke kokarin gani shugaba Kiir da jagoran 'yan tawaye Reik Machar sun kafa gwamnatin hadaka wadda za ta kasance a matakin rikon kwarya, kafin zabe.
Yanzu dai 'yan tawayen sun fara kiran Kiir shugaban mulkin kama karya duk da hujjar da magoya bayansa suka bayar, na cewa an yi hakan ne dan gudun barin gibi a madafun iko, bayan da tattaunawar sulhun ta rushe, amma tabbas zai cigaba da neman hanyoyin sulhu.
Dama dai ranartara ga watan Yuli mai zuwa ne aka sa ran yin zabe a kasar da ke fama da rarrabuwar kawuna