Baraka tsakanin 'yan tawayen Sudan ta Kudu
July 23, 2016Talla
Wata baraka ta kunno kai a cikin tsohuwar kungiyar tawayen Sudan ta Kudu, inda kusoshinta suka nada daya daga cikinsu domin ya maye gurbin Riek Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa. A lokacin da ya yi jawabi bayan da suka gudanar da taro a wani Otel da ke birnin Juba, Ezekiel Lol Gatkuoth ya ce sun amince Taban Deng Gai ya zama mataimakin shugaban kasa.
Shi dai Riek Machar ya gudu daga Juba babban birnin kasar, tun bayan barkewar kazamin fada da aka gwabza tsakanin dakarun shugaba Salva Kiir da na 'yan tawaye makonni biyun da suka gabata. Sai dai kafin ya arce, Machar ya sauke Taban Deng Gai da aka nada don ya gajeshi a mukaminsa na minista.