Barazanar kungiyar IS a kasar Libiya
February 2, 2016Talla
Masu ikirarin jihadin na IS a Libiya dai da ke rike da birnin Syrte, na amfani ne da yanayin da kasar ke fuskanta na rashin tsayayyar gwamnati inda sau tari suka kai hare-hare ga ma'aikatun man kasar. Da yake magana kan wannan batu na kasar Libiya, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da ke halartar wani zaman taro a birnin Roma na kasar Italiya, ya ce a daidai lokacin da ake daf da samun gwamnatin hadin kan 'yan kasa, bai kyautu ba a ce 'yan jihadin kasar ta Libiya sun kai ga samun biliyoyin dalar Amirka daga man da suke sata ba.