1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Bashi na barazana ga ayyukan raya kasa a Najeriya

October 12, 2023

A karo na biyu cikin shekaru 20, Najeriya na neman hukumomin kudi na duniya su yafe mata bashin da ke barazanar kai ta karkashin kasa, A yanzu haka ma ta koma cin bashi da nufin biyan bukatun miliyoyin al'umma ta kasar.

https://p.dw.com/p/4XSRM
Jirgin kasa na zamani irin na Legas ya kasa samuwa a Najeriya sakamakon bashi
Jirgin kasa na zamani irin na Legas ya kasa samuwa a Najeriya sakamakon bashiHoto: Tope Ayoku/dpa/XinHua/picture alliance

Ya zuwa watan Yunin 2023, yawan bashin cikin gida da na kasashe da kungiyoyin waje ya haura Dalar Amurka miliyan 103, adadi mafi girma a cikin tarihin Najeriya. Wannan gammon bashin na barazana ga rayuwa da makomar al'ummarta da ake kokarin wadatawa da hanyoyi ya zuwa titin jirgi tare da inganta lafiyarsu, lamarin da ya tilasta wa masu mulki jagorantar wata sabuwar gwagwarmaya ta neman afuwar bashi ga kasashen nahiyar Afirka.

Karin bayani:Bashi ya yi wa Najeriya katutu 


Karkashin wata kungiyar kasashe 24, ministan kudi na tarrayar Najeriyar Wale Edun ya ce ko bayan ahwuar mai tasiri, kasashen nahiyar na da bukatar kara musu wani sabon bashin da ke da tasiri a kokarin ginin kasashensu. Labarin bashin na zaman maras dadi da ke barazanar shake wuyan kasashe na nahiyar da daman gaske ciki har da Zambiya zuwa ga Malawi da ita kanta tarrayar Najeriyar da ke a kan gaba.  

Kudin gudanar da ayyukan raya kasa sun yi wa gwamnatin Najeriya karanci
Kudin gudanar da ayyukan raya kasa sun yi wa gwamnatin Najeriya karanciHoto: Ubale Musa/DW

Karin bayani:Najeriya za ta ciwo bashi

90% na daukacin kudadn shigar tarrayar Najeriyar na tafiya ne bisa kudin ruwar bashi. Wata kididiga ta babban bankin kasar na CBN ya fitari ta ce Najeiryar ta kashe kusan dala miliyan 2,000 a watanni bakwai na farkon 2023 a neman biyan kudin ruwan bashin nata. A tunanin Faruk BB Faruk da ke sharhi kan siyasa da ci-gaban al'umma, da kamar wuya tarrayar Najeriyar ta yi nasarar kaiwa ya zuwa ga lamuni a cikin tsarin kisan kudi maras tsari a bangaren 'yan mulkin Kasar

Karin bayani:Najeriya: Kasafin kudin badi sai da bashi  

Mafi yawa na ayyukan da masu mulki na Najeriya ke ikirarin ci musu bashin na neman komawa ayyuka irin Babangiwa. Daruruwan ayyuka da ke da hoton bashin sun gaza kamalluwa balle a samar da moriya ga 'yan kasar kama daga hanyoyi ya zuwa layin dogo da uwa uba wutar lantarki. Dr Isa Abdullahi da ke zama kwarrare a fannin tattalin arziki ya ce daukacin bashin da ke cikin kasar ya isa kaiwa ga biyan bukata.  

Babban bankin Najeriya ya dauki matakan inganta tattalin arzikin Najeriya
Babban bankin Najeriya ya dauki matakan inganta tattalin arzikin Najeriya

Karain bayani:Shirin mika mulki cikin rashin kudi

Tarrayar Najeriyar ta ci moriyar lamunin a can baya inda a shekarar 2006 ta biya dalar Amurka miliyan dubu 18 kan hanyar lamunin da ya kai na dalar Amurka miliyan dubu 40 da doriya. Sai dai ta sake tara wani sabon bashin da ya haura dala miliyan dubu 100 cikin tsawon shekaru 17, a wani abin da ke kama da kokarin sa hannu na 'yan uba cikin harkokinta.