Batun mayar da Charles Taylor gida
March 13, 2006Talla
Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya tattauna da takwaransa na Afrika ta Kudu Thabo Mbeki game da batun mayar da tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor gida.
Kakakin gwamnati Remi Oyo ta bayyana haka koda yake bata kara wani bayani game da ziyarar da Mbeki ya kai wa Obasanjo ba a daren jiya, amma majiyoyi daga Laberiya sun fadi tun farko cewa Obasanjo zai tattauna da shugabanin Afrika kafin mika Taylor ga kasarsa.
A watan Agusta na 2003 ne dai Obasanjo da Mbeki suka shawo kan Charles Taylor ya sauka daga mulki ya kuma amince da zaman mafaka a Najeriya, a kokarinsu na kawo karshen yakin basasa ba shekaru 14 a kasar ta Liberia.