Rikicin makiyaya a Afirka ya dauki hankali jaridun Jamus
May 11, 2018(Za mu fara da sharhi da labarun jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan mako ta duba matsalar makiyaya a nahiyar Afirka tana mai cewa ana kara nuna wa makiyaya a Afirka kyama.Ta ce a kasashen yankin Sahel rikici tsakanin manoma da makiyaya na kara yin muni. Jaridar ta ba da misali da arewacin Najeriya da ma wasu yankuna na kasar inda ta ce makiyaya na kara fuskantar matsin lamba. Kwararowar hamada ta sa ala tilas makiyayan na kaura zuwa kudu, sai dai a kudun mamnkarancin filayen kiwo da karuwar yawan al'umma na zama babbar matsala da ke janyo tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma.
Gazawar shugabannin na samar da da hanyoyin magance matsalar ta rikicin manoma da makiyaya
Da ga kuma bangaren shugabannin siyasa har yanzu ba wani mataki na a zo a gani da ake dauka don kawo karshen rikicin. Jaridar ta kara da cewa dole a bullo da sabbin dubarun kiwo, musamman samar da filaye na kiwo ga makiyaya don rage yawa yawan tashin hankali tsakaninsu da manoma.
Kasashen Afirka da dama na fama da matsalar rashin kudin gudanarwa, a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, inda ta kara da cewa bayan an yafewa kasashen Afirka basussukan da ke kansu a baya, da yawa daga cikin kasashen sun sake karbar bashi masu yawan kudaden ruwa, lamarin da ya zame wa kasashen alakakai, kuma da yawa daga cikinsu na fuskantar barazanar rugujewa saboda karancin kudi.
Matsalar rashin kudi ta yi kamari a ciki har' da Sudan inda gwamnatin ta gaza biyan albashi
Kasar Sudan wadda ta yi fama da takunkumin karya tattalin arziki na tsawon shekaru, daya ce a cikin kasashen na Afirka da ke fama da rashin kudi, inda ta kwashe watanni da yawa ba ta iya biyan albashin jami'an diplomasiyyarta, hatta kudin hayar gidajensu ma ta kasa biya. A halin ma da ake ciki wasu daga cikin jakadunta sun koma gida don radin kansu. Sai dai ba Sudan kadai ke fama da matsalar karancin kudin ba, wasu kasashen Afirka ma dai na fuskantar barazanar durkushewa saboda rashin kudi. Daga cikin kasashe shida da Asusun IMF ya ce suna da wannan matsala, biyar suna a nahiyar ta Afirka. Baya ga Sudan akwai Sudan ta Kudu mai fama da yakin basasa, da Chadi da Mozambik da kuma Zimbabuwe.Tsohon shahararren dan wasan tenis na duniya kuma dan kasar Jamus Boris Becker ya fara wani aiki mai wahala a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inji jaridar Berliner Zeitung. A makonnin baya kasar ta nada Boris Becker a matsayin wakilinta na musamman a harkokin wasannin motsa jiki. Shi kuma a nashi bangare tsohon tauraron wasan tenis ya yi alkawarin amfani da alakarsa da kungiyoyin wasanni na duniya da dangantakarsa wajen kawo zaman lafiya da rayuwa mai inganci a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da al'ummarta. Sai dai da wuya wai gurguwa da auren nesa, in Becker wanda shi kanshi ke fama da matsaloli na kudi zai iya cika wannan alkawari, domin har yanzu kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fuskantar barazanar fadawa wani sabon yakin basasa.))