Batun 'yan aware a Kamaru ya dauki hankalin jaridun Jamus
May 4, 2018Za mu fara sharhin jaridun na Jamus da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta yi tsokaci kan halin da ake ciki a yankin da ke amfani da harshen ingilishi na kasar Kamaru tana mai cewa rikici ya yi tsamari a yankin da ke son ballewa na kasar Kamaru rikicin da ke da alama da yakin basasa. Jaridar ta ce makonni biyu da suka wuce an kai wani hari a wani kauye da ke kudu maso yammacin Kamaru inda aka kashe mutane da dama wasu daruruwa suka tsere kana aka yi kone-kone. Rahotanni sun saba wa juna kan wanda ke da alhakin kai harin, yayin da wasu ke zargin 'yan tawaye da hannu wasu kuma sojoji suka dora wa laifin. Jaridar ta ce rikici a yankin na masu amfani da Ingilishi a Kamaru na kara rincibewa, lamarin kuma da ke barazanar rikidewa zuwa yakin basasa. Har yanzu mutane kalilan ne suka yi amanna za a iya kawo karshen rikicin cikin kankanen lokaci. Sai dai an ba da shawarar a shigar da cocin Katholika a kokarin neman yin sulhu tsakanin gwamnatin Shugaba Paul Biya da 'yan awaren.
Babu alamun wani babban sauyi a Zimbabuwe
Daga Kamaru sai kasar Zimbabuwe, inda jaridar Neues Deutchland ta ce fiye da kwanakin 100 ke nan da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya fara jan ragamar mulki, inda yake kokarin shawo kan masu zuba jari a kasar. Tuni dai sabon shugaban ya fara aiwatar da sauye-sauye da sabbin dokoki bisa manufar kawo sauki ga masu sha'awar kafa masana'antu. Sai dai wasu 'yan kasar ta Zimbabuwe musamman ma 'yan siyasa na bangaren adawa sun nuna shakku cewa karkashin Shugaba Mnangagwa da ya taba kasancewa mataimakin Shugaba Robert Mugabe da Constantino Chiwenga a matsayin hafsan hafsoshin kasa da wasu ma'aikatu a cikin wannan gwamnati ba bu wasu sauye-sauye na hakika da za a gani. Bayan kawo karshen mulkin tsawon shekaru gommai na Mugabe, da yawa daga cikin 'yan kasar ta Zimbabuwe sun yi kyakkyawan fata na samun sauyin a zo a gani, kuma har yanzu wasu na da wannan fata.
Noman Koko a Cote d'Ivoir da Ghana
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon labari ta buga game da harkar cinikin cakulet da ke kara bunkasa musamman a kasashe masu ci gaba. Jaridar ta fara ne da cewa, ci da gumin mutane da ya yi kama da bauta. A kasashe irinsu Cote d'Ivoire da Ghana da ke da arzikin koko, manoman koko din wanda da shi ake cakulet na fama da talauci. Amma ainihin kudin ana samunsu a kasashe masu ci gaban masana'antu, inda wasu kamfanoni kalilan ake cin amfaninshi. Su kuwa manoma a Afirka na tashi hannu banza, kuma har yanzu ba bu alamun halin da suke ciki zai canja. Tushen matsalar dai ba a kan faduwar farashin kokon a kasuwannin duniya da manyan kamfanonin kasashen yamma ba ne kawai. Wani bangane na matsalar na a kan kasashen Afirka kamar Ghana wadda ta shafe shekaru gommai ba ta yi amfani da kudin da take samu wajen kafa masana'antun da za su sarrafa danyen kokon ba. Sannan ba bu wata tattaunawa tsakanin kasashe masu noman kokon.