1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Benin ta janye haramcin da ta yi wa Nijar na fiton kayayyaki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 28, 2023

Haramcin fiton kayayyakin Jamhuriyar Nijar ya janyo wa Jamhuriyar Benin asarar tarin kudaden shiga

https://p.dw.com/p/4ae4A
Hoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

Jamhuriyar Benin ta janye haramcin da ta yi wa Jamhuriyar Nijar na jigilar kayayyakinta ta gabar ruwan birnin Cotonou, kamar yadda darakta janar na hukumar kula da shige da ficen kayayyaki ta ruwan kasar Bart Jozef Johan Van Eenoo ya sanar a Larabar nan.

Karin bayani:Benin za ta bude kan iyakarta da Nijar

Haramcin fiton kayayyakin Jamhuriyar Nijar ya janyo wa Jamhuriyar Benin asarar tarin kudaden shiga.

Karin bayani:Tashar ruwa ta Cotonou ta daina karbar hajoji da ke zuwa Nijar

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ce ta kakabawa Nijar din takunkumin sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata, inda suka hambarar da gwamnatin Dimokuradiyya ta Mohamed Bazoum.