1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubale ga Netanyahu a zaben Isra'ila

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 18, 2019

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa ba zai halarci taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a birnin New York na Amirka ba.

https://p.dw.com/p/3PpEG
Bildkombo:  Benny Gantz, Avigdor Lieberman und Benjamin Netanyahu
Gwamnatin hadaka a SaudiyyaHoto: Reuters/R. Zvulun

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu dai ya saba halartar wannan taron da kuma kara gabatar da muradun Isra'ilan ga duniya. Matakin dai na zuwa ne jim kadan bayan kammala zaben 'yan majalisu wanda Netanyahun ya gaza samun nasarar da za ta ba shi damar kafa gwamnati. Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyar da ake gudanar da zabe a Isra'ilan, bayan da cikin watan Afrilun wannan shekarar jam'iyya mai mulki ta Lukud ta gaza kai bantenta a zaben da aka gudanar a wancan lokaci. A yanzu dai tilas a kafa gwamnatin hadaka, wanda hakan zai bai wa Firaminista Benjamin Netanyahu karkashin jam'iyyar Lukud ko kuma abokin hamayyarsa da suka yi kunnen doki da shi tun a karon farko Benny Gantz na jam'iyyar Blue and White damar zama Firaminista. Sai dai hakan zai tabbata ne kawai da goyon bayan Avigdor Lieberman na jam'iyyar Yisrael Beiteinu, da tun da farko yaki bai wa Netanyahu goyon baya a zaben watan Afrilun da ya gabata.