Benny Gantz zai kafa gwamnatin Isra'ila
March 16, 2020Talla
Wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar Isra'ila ta bayyana cewa 'yan majalisa 61 sun kada kuri'ar amincewa da Benny Gantz a matsayin wanda ya fi cancanta ya kafa sabuwar gwamnati, yayin da firaminita mai ci yanzu Benjamin Neatnyahu ya samu kuri'u 58.
Wannan kaye da Firaminista Netanyahu ya sha bai zai kawo karshen mulkinsa ba, domin shugaban kasa Reuven Rivlin ya yi kira ga bangarorin da ke hamayya da juna da su kafa gwamnatin hadin gwiwa, domin kawo karshen rikicin siyasa da aka shafe watanni ana fuskanta a Isra'ila sakamakon rashin samun rinjaye a majalisa.
Babban kalubalen da ke gaban sabon majalisar ministocin Isra'ila dai shi ne annobar Corona wacce ta kama 'yan kasar 250.