1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na neman kama shugaban al-Shabaab

Mouhamadou Awal Balarabe
January 5, 2023

Amirka ta yi tayin bayar da tukuicin dala miliyan 10 ga duk wanda ya kama wani shugaban kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya, wanda ake zargi da kai hari a sansanin sojojin Amirka da ke Kenya.

https://p.dw.com/p/4LnTP
Joe Biden a lokacin da ya kai ziyara birnin Nairobi na GhanaHoto: DAI KUROKAWA/Epa/dpa/picture alliance

Shekaru biyun da suka gabata ne wani kwamandan Shabaab ya kai wannnan mummunan harin da ya yi sanadin mutuwar Amirkawa uku a sansanin. A cewar wani bincike da jami'ar George Washington ta gudanar a shekarar da ta gabata, Jaysh Ayman, kwamanda na kungiyar ta al-Shaabab ne ya kutsa Kenya don kai wannan hari.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amirka ta yi shelar cewa wannan tukuicin zai shafi hatta wanda ya bayar da bayani da ya kai ga kama Jaysh Ayman, kwamanda na al-Shaabab. Kungiyar ta al-Shaabab mai alaka da Al-Qaeda na yakar gwamnatin Somaliya da ke samun goyon bayan kasashen duniya. Amma tun a shekarar 2008 ne fadar mulki ta Washington ta sanya a sahun kungiyar ta'addanci.