Shugabannin Amirka da Rasha na ganawa
June 16, 2021Talla
Ana sa ran wanan ganawa za ta saka ruwan sanhi na jiyoyin wuyar da ake yawan tadawa a 'yan kwanakin baya-bayan nan tsakanin manyan kasashen duniyar guda biyu. Batutuwan da ake samun sabanin a kai tsakanin Amirka da Rashar suna da yawa, sai da abin da zai fi daukar hankali shi ne batun Ukraine da Belarusiya da kasashen ke yin takaddama a kai.