SiyasaAfirka
Amirka ta dawo da tallafin Falisdinu
April 8, 2021Talla
Shugaban Amirka Joe Biden ya sanar da dawo da tallafin da kasar ke bai wa Falasdinawa. Shekaru uku bayan dakatar da tallafin kudin na shekara shekara da gwamnatin tsohon Shugaban Amirkan Donald Trump ta yi, gwamnatin Shugaba Biden ta sanar da dawo da bai wa Falasdinawan wannan tallafin da ya kai dala miliyan dari hudu (400) a duk shekara.
Gwamnatin ta Biden dai, ta ce ta dauki wannan matakin ne don karfafawa Falasdinawa guiwar komowa kan teburin tattaunawar zaman lafiya da makwabciyar kasar Isra'ila. Al'ummar yankin Falisdinu sun fuskanci kuncin rayuwa a tsawon wadannan shekarun da aka dakatar da tallafin kudaden ga yankin da ke fama da tashe-tashen hankula.