1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a Abuja

Ubale Musa / LMJDecember 16, 2015

Shugabannin kasashen yankin Yammacin Afirka 15 na can a Abuja suna bikin cikar kungiyar bunkasa ci-gaban tattalin arziki ta yankin Yammacin Afirkan shekaru 40 da kafuwa.

https://p.dw.com/p/1HOnl
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAOHoto: AFP/Getty Images

Ko bayan share tsawon shekarunsu 40 suna fama da kawance, taron dai na zaman dama ta murnan kamalla zabuka a wasu kasashen yankin guda biyar ba tare da tashi na hankalin da aka tsammata tun daga farkon fari ba. Abun kuma da ya mai da taron na Abuja damar balle kwalba dama rawar Owambe a tsakanin shugabanni na kasashen yankin 15. Shugabannin dai suna shirin share tsawon kwanaki biyun da ke tafe domin nazarin nasarori dama kalualen da ke gaba na kawancen da aka faro shi a shekarar 1975 amma kuma ya kasa kaiwa ga gammaya har yanzu. Babban buri tun daga farkon fari dai na zaman samar da hadadden yankin ciniki a tsakanin kasashen yankin dake zaman renon Ingila da Faransa dama wadanda Potugal ta raina can baya. To sai dai kuma duk da irin nasarorin da suka mamaye shekarun na gamayya, a kan gaba har ya zuwa yanzu na zaman babbar matsalar rashin tsaron da ke zaman ruwan dare game duniya a yankin.

Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Rashin tsaro da talauci da fatara

Ko bayan nan sai matsalalon fatara da talauci da sukai katutu a rayuka na kusan kaso 70 cikin dari na al'ummar yankin da kuma ake ta'allakawa da karuwar ta tashi na hankali a tsakanin yan yankin. Matsalolin kuma da a fadar shugaban Tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari da ke zama mai masaukin baki ke zaman babbar barazana ga makomar yankin yanzu:

"Duk da muhimman ci-gaban da muka samu, har yanzu al'ummarmu na fuskantar manyan matsaloli. Wasunsu na barazana ga kokari na gamayyarmu, wasu kuma sun shafi tsaro da zaman lafiya dama siyasar yankin. Akwai kuma muhimman matsalolin mulki tafi da harkokin hukumar gudanarwar yankin da ke da bukatar nazarin gaggawa. Matsalolin tsaro na ci gaba a cikin yankinmu, haka kuma muna fuskantar aiyyuka na 'yan kwaya, dillanci na makamai da fashi na jiragen ruwa da dukkanninsu ke zaman barazanar tsaro a cikin yankin. Ko bayan nan kuma akwai matsalar karin tsagerancin addini da matsala ta ta'ddanci. Duk wadannan na zaman babar barazanar da ke bukatar hankalinmu da hannunmu."

Bayan matsaloli akwai nasara

To sai dai kuma jerin matsalolin ba su dauke hankali na shugabannin da ke kallon shekarun 40 na ECOWAS a matsayin babbar nasara ga 'yan yankin miliyan 250 a fadar Macky Sall da ke zaman shugaban kungiyar a halin yanzu kuma shugaba ga kasar Senegal:

Shugaban kasar Senegal kana shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO Macky Sall
Shugaban kasar Senegal kana shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO Macky SallHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

"Duk da cewar dai ba a kai ga cika burin na gamayya ba har ya zuwa yanzu, yankinmu na samun gaggarumin cigaba musamman ma ga batun noma, da ciniki dama kokarin hada kan al'ummarmu."

Taron na Abuja dai na zama damar saka danbar wasu shekaru 40 cikin jin dadi da annashuwa, ga al'ummar yankin da sannu a hankali ke dawowa daga rakiyar shugabannin sai baba ta gani dama bude ido a bisa tabbatar da cigaban al'umma.