Bikin rantsar da shugabar ƙasar Brazil
January 1, 2011Mace ta farko da aka zaɓa shugaban ƙasa a Brazil wato Dilma Rossef ta yi rantsuwar fara wa'adin mulki na shekaru huɗu a ƙasar da ta fi samun bunƙasar tattalin arziki a yankin latine Amirka. Madame Roussef mai shekaru 63 a duniya ta yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana ranar 31 ga watan oktoba sakamakon goyon bayan da ta samu daga shugaba Lula da sylva mai barin gado, da doka ta haramta masa tsayawa takara.
Shugabanni ƙasashe 47 da suka fito daga yankin latine Amirka da kuma afirka ne suka halartarci bikin rantsarwar a birnin Braziliya. Sakatariyar harkokin wajen Amirka wato Hilary Clinton itace ta wakilci ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a duniya. Daga cikin sauye sauye da ake sa ran Dilma Roussef za ta kawo a ƙasar ta Brazil, har da rage kuɗin da gwamanti ta ke amfani da shi wajen gudanar da hidimominta, tare kuma da ƙara wa ma'aikatan gwamnati albashi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala