1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Musulmi na bikin Sallah

April 23, 2023

Al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kamar sauran sassan duniya, sun gudanar da bikin Sallah Karama ba tare da wata barazanar tsaro ko wani tashin hankali ba.

https://p.dw.com/p/4QPQQ
Shagulgulan Sallah Karama
Shagulgulan Sallah KaramaHoto: Adeyinka Yusuf/AA/picture alliance

An gudanar da Sallah lami lafiya a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno ba tare da fargaba ko zullumi ba, idan aka kwatanta da yadda ya ke a shekarun baya da aka yi ta fama da matsalar tsaro. A bana, mutane sun fita zuwa Masallatan Idi cikin sabbin kaya da annashuwa da fara’a. A jihohin Gombe da Yobe ma an yi Sallar cikin kwanciyar hankali, mutane sun yi farin cikin yadda aka gudanar da sallah ba tare da samun rarrabuwar kai kamar yadda lamarin yake a baya ba.

A jihohin Gombe da Yobe ma, an ci gaba da gudanar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali. Mutane sun yi farin cikin yadda aka yi ba tare da samun rarrabuwar kai kamar yadda lamarin yake a baya ba.

A Jamhuriyar Kamaru ma dai a wannan Jumma'a, al'ummar Musulmi na kasar suka gudanar da bukukuwan karamar sallar, kuma a lokacin da aka kamalla sallar idi, sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma, sun ja hankalin jama'a kan kyautata zamantakewa aure da mu'amala da kuma karfafa zaman lafiya la'akari da halin da duniya ta fada na rikice-rikice.