Bincike kan kisan kai a Sudan ta Kudu
April 22, 2014Galibin mutanen da aka hallaka wanda suka ka tasamma 200 sun gamu da ajalinsu ne lokacin da wasu 'yan tawaye suka karbe garin nan na Bentui da ke da arzikin man fetur, inda suka yi ta zakulo wadandan ke adawa da su suna kashe yayin da a hannu guda suka yi ta shela a kafafen watsa labarai na maza su yi wa matan da ke kabilar da ba ta 'yan tawayen ba fyade.
Tuni dai aka fara zargin wandanda ke biyayya da shugaban 'yan adawar kasar Riek Machar da aiwatar da wannan kisa, sai da tuni Mr. Machar din ya musanta wannan zargi.
Kasashen duniya gami da kungiyoyi na kare hakkin bani Adama sun nuna takaicinsu dangane da yadda ake yin amfani da kabilanci ko banbanci na siyasa wajen tafka irin wannan danyen aiki.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu