Birtaniya ta mika takardar barin EU
March 29, 2017Birtaniya a hukumance ta mika takardar shirin barin Kungiyar Tarayyar Turai EU a wannan rana ta Laraba, inda aka mika takardar barin wannan kungiya ga Shugaban Kungiyar ta EU Donald Tusk kamar yadda Firaminista Theresa May ta bayyana a gaban majalisa:
"Babban jakadan Birtaniya zuwa ga Kungiyar EU a madadina ya mika matsayar gwamnatin Birtaniya abin da zai motsa yarjejeniyar Kungiyar EU mai lamba 50. Lamarin da ke nuna cewa al'ummar Birtaniya sun daura damba ta aiwatar da aniyarsu ta barin Kungiyar ta EU."
Tim Barrow, jakadan Birtaniya a Kungiyar ta EU shi ya mika wannan takardar ta fara shirin fita daga EU wacce Firaminista Theresa May ta rattabawa hannu a kanta, ya kuma mikata ne ga Tusk a ofishinsa da ke birnin Brussels.
Da ta ke mayar da nasu martani kan ficewar ta Birtaniya daga EU Ulrike Demmer mai magana da yawun Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Birtaniya za ta ci gaba da kasancewa kawa ga kungiyar ta EU da ma Kungiyar tsaro ta NATO.