Za a mayar wa Najeriya kayan tarihi
May 11, 2021Lokacin da dakarun 'yan mulkin mallaka nA Birtaniya suka mamaye tsohuwar Daular Benin ta Najeriya a 1897 sun yi awon gaba da dubban kayayyaki kira na gargajiya na tarihi masu daraja wadanda wasun su a yau ake samunsu a cikin gidajan ajiye kayan tarihi na Birtaniya. Misali jamia'ar Abeerden da ke a Birtaniyar tana rike da wani abun rufe fuska dan madundumi ko Facemask da aka sato daga gidan sarkin tsofuwar daular ta Benin wanda yanzu take son ta mayar da shi.
Wasu a gidajan tarihi na tsofin shugabanin yan mulkin mallakar, wasu a ckin jami'o'i Neil Curtice shi ne daraktan gidan ajiye kayan tarihi na jami'ar Aberdeen.
"An sace kayayyaki an yi wasosso kuma kayayyakin da aka saton bai kamata ba a ce sun zama mallakar jami'ar mu ba.
Abun rufe fuskar na gidan sarautar ta tsofuwar daular ta Benin, wadanda suka kasance jagororin jami'ar ta Aberdeen sun sayeshi a shekara ta 1957 a wani wantaran da aka yi kudi tsaba Fam 750 wanda a yanzu ake ajiye da shi a gidn addana kayan tarihi na jami'ar ta Aberdeen. Kusan shekara guda ke nan da ake tafka muhawara a game da irin taadin da 'yan mulkin mallaka na Birtaniya suka aikata a nahiyar Afirka na yin fashi a game da kayan tarihin kamar su dan butuntume, gumaka na zinari da azurfa da sauran kadarori.
Dan Hicks ma'aji a gidan ajiye kayan tarihi na Pitt Museum da ke a Oxford ya ce dira mkiya da da sojojin mulkin mallakar suka yi a 1897 a Benin sun wasashi abubuwa da dama.
''Tabbas an bi didigi tun daga farko har karshe na kayayyakin da ake da su a lokacin a masarautar kafin suka yi awon gaba da su. An yi musu kwace na addini da 'yanci da kuma al'adu
Bayan jami'ar Aberdeen akwai wasu jami'oi Birtaniyar da suka sanar da sake mayar a kayyayakin na tarihi da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya sukasato. Misali Cocin Anglikan tana son sake mayar da wasu butuntumi guda biyu na tagulla wadanda ta samesu shekau 40 da suka wuce.
Yayin da wani kamfannin sayar da kayayyakin wantare ya janye irin kayyakin tarihin da aka sato daga Benin daga cikin kayan da yakan sayarwa, Hicks ya kara da cewar.
"Yadda muka yi aka sake dawo da kayyaykin da yan mlkin Nazi suka wasashe ya kamata mu yi haka a game a irin sace-sace da aka yi a tsofuwar daulr Benin ta can dauri".
Alkaluma sun nuna cewar gidan ajiye kayan tarihi na British Museum ya fi kowanne daga cikinsu yawan kayayyyakin da aka sato daga tsofuwar Daular Benin da ke kudancin tarayyar Najeriya wanda aka kirga kayayyaki daya-daya har 928 wanda ta intanet ma ake iya ganinsu.
Sai dai ya zuwa yanzu babu alamun gidan ajiye kayan tarihin na Birtaniya ko yana da niyyar sake mayar a kayayyakin tarihin duk da ma cewar ya amince da cear na sata ne.