1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Matsalar biyan kudin fansa a Najeriya

December 18, 2024

Wani rahoto hukumar kididdiga ta Najeriya ya ce 'yan kasar sun biya kudin fansa ga 'yan bindiga sama da naira tiriliyan biyu. Hukumar ta ce an biya kudin fansar tsakanin watannin Mayun Shekarar 2023 zuwa Afrilun 2024.

https://p.dw.com/p/4oJX6
Kasuwa a jihar Katsina da ke Najeriya
Kasuwa a jihar Katsina da ke NajeriyaHoto: AFP

Rahotan kididdigar ya nuna Arewacin kasar yafi jikata wajan biyan kudin fansar inda aka biya jiblar naira tiriliyan daya da milliyan 81.Inda kudincin kasar suka biya jiblar naira milliyan 424 da milliyan 27. Rahoton dai ya ce mafi akasarin kudin mutanan yankunan karkara ne suka biya su abin da ya sa al'umma irin su Sanusi Ibrahim ci gaba da martani wanda ya ce abin bai ba su mamaki ba.

Karin Bayani: Sabbin matakan tsaro a Jihar Sokoton Najeriya

Najeriya | Bayan garkuwa da yara
Bayan garkuwa da yara a NajeriyaHoto: AP/dpa/picture alliance

Gwamnatin Najeriya dai ta haramta biyan kudin fansa ga al'ummar kasar sai dai kuma ba ta magance yin garkuwa da mutane ba, abin da ya sa Bala Yaro Mada dan jihar Zamfara ke cewa ya kamata a dau mataki. Wannan rahoto dai na hukumar kididdigar ya ce baya ga biyan kudin fansa da 'yan bindiga suke karba kuma wannan matsala ce da ta shafi birane da kauyuka inda cikin shekara guda masana na cewa tun da har hukumar gwamnatin kasa ta ba da wannan rahoto to za a saka ido aga matakin da za a dauka na magance afkuwar hakan nan gaba.