Bobi Wine dan adawa ya fice daga Yuganda
September 1, 2018Talla
Lauyan mawakin ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wannan Asabar. Mawakin na Reggae wanda aka fi sani da suna Bobi Wine ya bata lokaci a ranar Juma'a kafin barin asibitin gwamnati bayan da aka sake tsare shi a lokacin da yake kokarin barin asibiti.
Kyagulanyi ko Bobi Wine dai ya zama dan majalisa a shekarar 2017 inda ya rika jan hankalin matasa, abin da ke zama barazana ga Shugaba Yoweri Museveni. An dai kama shi ne a makon da ya gabata bisa zargin cin amanar kasa bayan da wasu gungun matasa suka jefi motar Shugaba Museveni na Yuganda.