1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: An hallaka sojoji 32 a Nijar

Salissou BoukariJune 4, 2016

'Yan Boko Haram sun kai hari a garin Bosso da ke cikin jihar Diffa mai makwabtaka da Tarayyar Najeriya inda suka hallaka sojoji 32 da jikkata wasu da dama.

https://p.dw.com/p/1J0bO
Nigeria Soldaten in Diffa
Hoto: Reuters/J. Penney

A kalla sojojin Nijar guda 30 tare da wasu sojojin Najeriya guda biyu ne suka rasu sakamakon gumurzu da suka yi da daruruwan 'yan Boko Haram da suka kai musu hari a garin Bosso da ke makwabtaka da Tarayyar Najeriya a cewar ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar.

Da yammacin Juma'a ne dai tun da wajejen karfe 6 da minti 50 'yan ta'addan na Boko haram suka kai harin ga sojojin da ke garin na Bosso inda hukumomin na Nijar suka ce wannan adadi na wucin gadi ne, domin wasu sojojin 67 na kasar ta Nijar da wani soja daya na Najeriya sun samu raunuka a cewar sanarwar ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar.