Boko Haram sun hallaka mutane a Niger
August 28, 2015Talla
Wasu mahara da a ke zargin mayakan Boko Haram ne sun kaddamar da hare-hare a wani kauye da ke a kudancin Niger, harin da yayi sanadin kisan mutane uku ciki kuwa har da soja a cewar majiyar jami'an tsaro a jiya Alhamis.
Harin da aka kai shi cikin dare a farkon makon nan ya faru ne a garin Abadam na yankin Diffa da ke iyaka da Najeriya.
A cewar wata majiya ta sojin Nijer harin da mayakan suka kai a daren ranar Talata ya yi sanadin kisan mutane biyu fararen hula sannan wani soja daya mai mukamin saja ya halaka a lokacin da dakarun sojan na Nijer ke fatattakar mayakan.
Wata majiyar ma ta tababbar wa 'yan jarida faruwar harin bisa sharudan ba za a bayyana sunansu ba.