Boko Haram ta kai hari a gabashin kasar Nijar
June 18, 2015Talla
Rahotanni daga Jamhuiriyar Nijar na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a daren Laraba a wasu garuruwa guda biyu da ke cikin jihar Diffa a gabashin kasar ta Nijar, inda suka kashe mutane akalla 30. Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke kai hari a wajan kasar Najeriya cikin mako guda, bayan harin da suka kai a ranar Litinin a birnin Ndjamena na kasar Chadi, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 34.