1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bom ya tashi da wasu jami´an yan sanda 13 a Iraq

Ibrahim SaniDecember 21, 2006

Rikice rikice a Iraqi na ci gaba da yawaita, wanda ya dara na ko wane lokaci yawa

https://p.dw.com/p/Btwx
Mr Bush da MR Rumsfeld
Mr Bush da MR RumsfeldHoto: AP

Ya zuwa yanzu dai rahotanni da suka iso mana daga kasar na nuni ne da cewa, wasu yan iRaqi 13 sun rasa rayukan su, sakamakon tashin wani bom a cibiyar daukar jami´an yan sanda dake birnin Bagadaza.

Jim kadan da tashin bom din a cewar bayanai jami´an yan sanda goma daga cikin 13, nan take suka rugamu gidan gaskiyar, kana ragowar ukun kuma sun karasa ne bayan da aka kaisu izuwa asibiti.

To sai dai kuma birigadiya Abdul Karim Khalaf dake lura da ayyukan jami´an tsaron na Iraqi, ya tabbatar da labarin faruwar wannan al´amari to sai dai kuma yace mutane 11 ne suka rasu, amma ba 13 kamar yadda wasu rahotanni suka ce ba.

Wannan hari a cewar rahotanni, na daga cikin hari na baya bayan nan ne da tsageru a kasar suka kaiwa jami´an tsaron kasar na Iraqi.

Bayan faruwar wannan al´amari, a waje daya kuma rahotanni sun nunar da rasuwar wasu mata fararen hula guda biyu a dai birnin na Bagadaza.

Hakan kuwa a cewar rahotanni ya faru ne bayan da aka harbo musu wasu rokoki lokacin suna cikin wata kasuwa dake kudu maso yammacin birnin na Bagadaza.

Faruwar rikice rikice irin wadannan abubuwa ne da za´a iya cewa sun kusan zamowa ruwan dare a kasar, domin koda a jiya sai da aka gano wasu gawarwaki 76,wacce ko wace gawa na dauke da tabo iri daban daban a jikinta, wanda hakan ke nuni da cewa kafin kisan mutanen sai da aka azabtar dasu tukuna.

Wani rahoto da hukumar tsaro ta Fentagon dake Amurka ta fitar a kwana kwanan nan na nuni ne da cewa tashe tashen hankula da kasar ta Iraqi ke fuskanta yanzu yafi na kowa ne lokaci yawa, a tsawon watanni uku da suka gabata.

A dai wannan hali da ake ciki,tuni kasar Amurka ta sanar da matakin kara yawan sojin ta a kasar ta Iraqi. Wadannan kalaman dai sun fito ne daga bakin shugaba Bush na Amurka,a indfa yaci gaba da cewa yan fadan sari ka noke dana kwanton bauna na cin dunduniyar sojojin Amurka a game da kokarin da suke na tabbatar da tsaro da oda a fadin kasar baki daya.

A dai watan janairun sabuwar shekara ne idan Allah ya kaimu ake sa ran shugaban na Amurka zai gabatar da sabon kudiri a game da manufofin Amurka game da kasar ta Iraqi.

Game kuwa da matakin karin sojin na Amurka a Iraqi, sabon ministan tsaron kasar wato Bob Gates yace yana nan yana tattauna wannan batu tare da wasu manya manyan askarawan sojin kasar don sanin matakin daya kamata a dauka.

Mr Gates wanda ya fadi hakan lokacin daya kai wata ziyarar gani da ido kasar ta iraqi, ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai ba zai ce komai ba game da karin sojin ko kuma akasin haka izuwa kasar ta Iraqi.