Boren adawa da sauyi ga sashen shari'ar Turkiya
February 26, 2014Dubun dubatan masu zanga zanga ne suka yi jerin gwano akan titunan Turkiya, bayan da shugaban kasar ya sanya hannu akan dokar da ta tsaurara iko akan sashen shari'ar kasar, wadda ta janyo cece kuce, a wani abin da ke karfafa rashin jin dadin da 'yan adawa ke nunawa gwamnatin da dama badakalar cin hanci ke ci gaba da dabaibayeta.
Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu boren a Ankara, babban birnin kasar, yayin da a birnin Istanbul kuwa, masu zanga zangar suka yi cincirindo a dandalin Taksim, wanda ke zama wurin da masu gangamin nuna adawa da gwamnati ke hallara daga lokaci zuwa lokaci na tsawon watanni kenan.
Jam'iyar adawa ta Republican People's Party (CHP) ce ta shirya gangami na karshe, bayan nadar muryar da ake zargin fira ministan kasar Recep Tayyip Erdogan na tattauna hanyar boye wasu makuddan kudade, zargin da kuma fira ministan ya kwatanta da cewar marar tushe ne, kuma ka'ge ne.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman