Boren kin jinin gwamnati ya karu a Sudan
February 28, 2023Talla
A zanga-zangar ta wannan Talata, an yi fito na fito tsakanin masu boren da jami'an kwantar da tarzoma na Sudan, inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare ma da harba albarusai da harsasan roba. Daya daga masu boren ya riga mu gidan gaskiya bayan da harsashi ya ratsa kirjinshi.
Kasar ta Sudan ta shiga cikin halin rashin tabbas tun bayan da sojoji suka hambarar da halartaciyar gwamnatin farar hula. A karshen shekarar da ta gabata ne, shugabannin soji da na farar hula suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rigingimun da suka mamaye Sudan tun bayan kifar da mulkin kasar.